Babban Bankin Nijeriya Ya Fara Sayar Da Takardun Kudin China — Leadership Hausa Newspapers

Sakamakon yarjejeniyar da a ka kulla a watan Mayun shekarar 2018 ta musayar kudi tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da Bankin Al’umma na kasar China (PBOC) za a fara sayar da kudin kasar ta China ga dillalan da a ka amince da su.
Idan za a iya tunawa, a cikin watan Mayu ne CBN ya rattaba hannun da bankin na al’umma na kasar China mai suna PBOC.
Yarjejeniyar za ta bayar da damar gudanar da kasuwanci a tsakanin kasashen biyu da kuma kara karfafa kudin musaya na kasar waje, inda wannan ya sanya Nijeriya ta zama ta uku a nahiyar Afrika bayan kasar Afrika ta Kudu da Masar, ita ma ta rattaba hannu da kasar da China.
Yarjejeniyar tsakanin bankunan biyu za ta bai wa kasashen biyu damar musayar kudi da su ka kai jimillar biliyan 15 ko Naira biliyan 720 ko kuma sama da haka a cikin shekaru uku masu zuwa.
Har ila yau, jarjejeniyar, za a iya kara fadada ta a bisa yadda kasashen biyu su ka amince.
Daraktan sashen kasuwancin kudi na CBN, Dakta Alban Ikoku, ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis da ta gabta, inda ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar ta musayar kudin zai bai wa bankunan biyu damar daukaka kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu ta hanyar saye da sayar da takardar kudi ta Yuan ta kasar ta China a bisa takardar kudi ta naira.
A cewar CBN, jarjejeniyar zata kuma yi amfani da ita wajen dorewa akan kasuwar kudi wadda aka sanya rai cewar bankunan zasu amince da hakan.
CBN ya kara da cewar, don samun dama shigar daukacin dillan da aka amince dasu a cikin harkar zasu bude asusu na Renminbi wanda ya yi daidai da bankin tare da kuma shawarar CBN itama tare da bayanan asusun ta na Renminbi wanda kuma zai iya kasancewa da banki na cikin gida ko na waje dake kasar China.
Wadanda suke da nufin shigo da kaya daga kasar China, zasu karbi takarda ta shigo da kaya a matsayin takardun da ake bukata na yin rijista don samar da kudin musaya na kasar waje na saye wanda ba wadda za’a yi amfani dasu bane wajen biya akan cinikayya ba wanda kuna wadanda zasu amfana ba daga kasar China suke fito ba.
A cewar CBN, dillan da aka amince baza su bude asusun banki wanda baya aiki ba a dikin asusun bankuna na masu yin ajiya ba.
Don cimma wadannan jarjejeniyar, dillalan da aka amince dasu zasu dinga ajiye kudi a bankuna da kuma bankunan ‘yan kasuwa.
A cewar CBN sayarwar ta renminbi, za’a dinga yin ta ne kawai don baiwa kasuwanci goyon baya ta hanyar cinikayya, inda bankin ya kara da cewa, masu shigo da kaya da kuma fitar dasu, zasu ci gaba da biya kudin tara akan kayan da aka shigo dasu da kuma kayan da aka fitar baki daya.
Dalilan da a ka amince da su, a na bukatar su tattala kudi a cikin awowi saba’in da biyu daga ranar da aka saba, haka kuma dole a dinga maido da kudin zuwa ga CBN don sake saye akan farashin na bankin.
CBN ya kuma sanar da cewar, zai dinga cirewa daga dillan da aka amince dasu a cikin babban asusun banki na ajiya a ranar da aka bayar da dauki wanda ya yi daidai da naira a bisa bukata ta renminbi.
CBN yana da ‘yancin kin sayarwa idan a ra’a yin sa ba’a bayar da farashin da for the don tabbatar wa a tsaknin takarfar naira da kuma takardar Yuan ta musaya wanda CBN zai iya zabar wani dauki babba na kasuwa ko sayarwa na kudi ko na gaba zaya.