CACOL Ta Bukaci EFCC Ta Yi Bincike Kan Zargin Badakalar Biliyan N500 A CBN — Leadership Hausa Newspapers

Cibiyar dake yaki da cin hanci da rashawa da gudanar da kyakyawan shugabanci CACOL, ta bukaci a gudanar da bincike akan labarin da aka buga a wata jarida na zargin badakalar kudi, sata da kuma tsakuda wasu kundin bayanan kudi kimanin naira biliyan 500 da aka kaisu zuwa kasar Dubai don zuba jari, amma sukayi batan dabo.

Shugaban Cibiyar ta CACOL Debo Adeniran a cikin sanarwar da ya fitar yace, “ Wasu sanannun jaridu ne suka ruwaito labaran na badakalar, inda Gwamnan Babban Bankin na CBN Godwin Emefiele da Mataimakin sa Edward Lametek Adamu da kuma Daraktan kudi Dayo M. Arowosegbe, harda wasu masu bayar da shawara ta musamman ga Babban Bankin na Nijeriya CBN Emmanuel Ukeje da akaji muryoyin su a cikin faifan bayanan suna tattaunawa akan yadda zasuyi rufa-rufa akan asarar da aka tabka ta sama da naira biliyan 500 da aka sace daga Babban Bankin Nijeriya CBN na jarin da aka zuba na musamman. “

Acewar jaridun na kafar yanar gizo, a tattaunawar da akayi ta wayar tafi da gidanka dake cikin faifan da kafar yada labarai ta yanar gizo ta Sahara Reporters ta samo, anji Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya CBN da kuma wasu manyan jami’an Babban Bankin na Nijeriya CBN suna tattaunawa akan kokarin soke asarar kudin zuba jarin na kasar Dubai kamar yadda watk majiya kusa da bankin ta labarto.

Anji Gwamnan na Babban Bankin Nijeriya CBN Mista Godwin Emefiele yana gayawa mataimakin sa Adamu a cikin faifan bayanan cewar, “Don a gujewa wata babbar matsala ya kamata gwamnati ta buzukaci amincewa ta bamu gundarin a kalla naira biliyan 100, sai dai kuma gwamnatin bazata amince da hakan ba. “

Faifan bayanan yana kunshe da muryoyin manyan jami’an na Babban Bankin Nijeriya CBN sun hada baki don yin rufa-rufa akan badakalar wacce tayiwa tattalin arzinin kasar nan nakasu.

Bugu da kari, a cikin bayanan na faifan, ana zsrgin anji muryar Gwamnan na Babban Bankin Nijeriya CBN Godwin Emefiele yana yin doguwar tattaunawa da wasu manyan jam’an bankin na Babban Bankin na Nijeriya CBN suna maganar a soke asarar masu ruwa da tsaki daga cikin bankunan kasuwanci da aka ruwaito cewar, an karkatar da zuba jarin na kasar Dubai da kudin ya kai naira biliyan 500 tun a wani lokaci a shekarar 2018.

Cibiyar ta CACOL tayi kira ga Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa guda biyu dake yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC da ICPC dasu gaggauta gudanar da bincike mai zurfi akan daukacin zarge-zargen don zakulo wadanda sume da hannu a ciki don kaucewa jefa tattalin arzikin kasar nan a cikin matsala.

Sai dai, mai magana da yawun Babban Bankin na Nijeriya CBN Issac Okorafor ya tabbatar da sahihancin faifan tattaunawar, inda ya yi ikirarin cewar, tattaunawa ce wadda dama an saba yinta a tsakanin manyan jami’an Babban Bankin na CBN sai dai, akwai barazana a cikin tattaunawar dake cikin faifan wanda baiyi daidai da zargin da akayi ba.