CBN Ya Raba Naira Biliyan 38 Ga Kamfanin Samar Da Wutan Lantarki A Cikin Wata Shida

CBN Ya Raba Naira Biliyan 38 Ga Kamfanin Samar Da Wutan Lantarki A Cikin Wata Shida

Babban Bankin Kasar nan CBN ya sanar da cewar, ya tura jimlar Naira Biliyan 38.53 ga Kamfanonin da ke samar da wutar lantarki daga watan Janiaru zuwa datan Yuni na wannan shekarar ta 2018 a karkashin kasuwanci dorewar wutar na NEMSF.
Bayanin hakan yana kunshe a cikin sabon rahoton da Babban Bankin na CBN ya fitar, inda Bankin ya ce, shi ne ya kirkiro da shirin a shekarar 2015 don a magance durkushewar fannin na samar da wutar lantarkin da kuma dorewar tattalin arzikin kasa.

A bisa bayani na hakika, shirin na NEMSF, Bankin ya kirkiro da shi ne don magance karancin samar da kudi shiga da kuma bin ka’idobin biyan bashin Gas ga wadanda suke a cikin kasuwancin.

Wadanda suke yin hada-hada a kamfanonin na samar da Gas, kamfanonin da suke samar da wutar, hukumar samar da wutar ta kasa TCN da kuma masu rabar da wutar.
CBN a cikin rahoton tattalin arzikin kasa, ya sanar da cewar, Naira Biliyan 38.53 din an rabar da ita ne ga kamfanin rabar da wutar guda daya, inda kuma kamfanin zai rabawarwa da kamfanoni sha bakwai da ke rabar da wutar da ga kamfanoni shida da ke rabar da Gas da kuma ma su samar wa guda biyar.

Bankin ya kara da cewa, a karshen watan Yulin wannan shekarar ta 2018, ya kai yawan Naira Biliyan 158.74 da aka rabar ga kamfanin da ke samar da wutar don bayarwa ga wadanda suke fannin da suka chanchanta.

Ya kara da cewa, Naira Biliyan 4.99 kudi be da aka sake biya da aka karba duk a cikin shekarar, inda jimlar ta kai kudin da aka sake biya ta kai yawan Naira Biliyan 20.56 tun a lokacin da aka fara.

Abewar rahoton, a zangon farkon tsakiyar shekarar 2018, an rabar da Naira Biliyan 38.53 ga kamfanin rabar da wutar guda daya don rabar wa fa kamfanoni samar da wutar sha bakwai da na Gas guda shidz kuma ma su rabar da wutar guda biyar.

Gaba daya a karshen watan Yuni, an rabar da Naira Biliyan 158.74 a cikin shekarar 2018 ga kamfanin NESISS don rabar wa da kamfanoni da suke samar da wutar guda talatin da bakwai da suka chanchnta su amfana.
Sakamakon daukin, Bankin zai samu damar samar da megawatts 1,193 daga madatsar samar da wutar guda goma da kuma mallakar karamar tashar samar da wutar guda daya.
Sauran mitocin wuta da aka samar sun kai yawan 414,000 da kuma taransfomomi guda 70,310 ma su karfi’ 500KBA da kamfanoni samar da wutar tare da gyara guda tarasfomomi ma su karfin 11KB da za su kai kilomita 332 da kuma layuyyukan wuta ma su karfin 0.45KB mai tsawon kilomita 130, harda kuma samarwa da gina sababbin kananan tashoshin wuta guda talatin da hudu.
Shirin na samar da karfin wutar an gudanar dasu ne a tashoshin samar da wutar, sai na samar da Gas guda goma a madatsun samar da Gas haka da na madatsun Geregu, Transcorp Ughelli da kuma na Ibom duk an gyara su.

Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN Mista Godwin Emefiele, a lokacin da yake yin jawabin sa a lokacin fara aikin ya sharci kamfanoni su yi amfani da kudaden yadda ya kamata don cimma burin da aka sa a gaba.
Acewar sa, kamfanonin samar da wutar da kuma na Gas, za su amfana da bashin, inda ya kara da cewar an rabar da kudin ne don inganta samar da wutar a kasar da kuma inganta kasuwancin da samar da mitoci da sauran kayan aiki.