Mun zuba jarin Naira biliyan 120 a masaku da masana’antun jima – CBN – Freedom Radio Nigeria

Mun zuba jarin Naira biliyan 120 a masaku da masana’antun jima – CBN – Freedom Radio Nigeria


Labarai

Published

on
Babban Bankin Kasa (CBN) ya ce ya zuba jarin Naira biliyan120 a harkokin masaku da masana’antun jima da sarrafa auduga.

Mataimakin gwamnan bankin na CBN, Mista Edward Lamatek Adamu ne ya bayyana hakan a jiya, ya yin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin masana’antun sarrafa auduga  a Abuja.

Bankin na CBN ya kuma ce a shekarar nan da muke ciki bankin yana kokarin noman auduga tan 300,000 don inganta masana’antun tufafi a kasar nan.

Mista Edward Adamu ya kara da cewa, kokarin da aka yi, ya haifar da karuwar masana’antun sarrafa tufafi a Najeriya.Post Views:
178

error: Content is protected !!